Duniya

Qatar Ta Tsayar da Fitar da Gas Yayin da Farashi Ya Tashi da Kashi 46%

Rikicin Gabas ta Tsakiya ya sake ɗaga hankulan kasuwannin duniya bayan da kasar Qatar ta dakatar da aikin fitar da iskar gas a yau Litinin, sakamakon hare haren da Iran ke kai wa kasashen Yankin Tekun Fasha. Matakin ya zo ne a rana ta uku da fara rikicin da ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran.

Qatar na samar da kusan kashi 20 cikin 100 na iskar gas da ake amfani da ita a duniya musamman ga kasuwannin Asiya da Turai abin da ke sa duk wata tangarda a aikinta ta zama babbar barazana ga daidaiton farashi a duniya.

Hari Kan Ras Laffan

Ana sa ran kamfanin man Qatar zai fitar da sanarwa kan matsalar da ta tilasta masa dakatar da aiki, bayan rahotannin cewa an kai hari kan matatar Ras Laffan cibiyar da ke tacewa da daskarar da iskar gas kafin jigilar ta zuwa kasashen waje. Masana sun ce duk wani tsaiko a Ras Laffan na da tasiri kai tsaye ga sarkar samar da makamashi ta duniya.

Saudiyya Ta Bi Sahun

Ba Qatar kaɗai ba ce ta fuskanci tangarda. Ita ma Saudi Arabia ta dakatar da aikin tace mai a babbar matatar ta da ke Ras Tanura, sakamakon hare-haren jirage marasa matuki da ake dangantawa da makaman Iran. Sai dai hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa matakin bai shafi aikin samar da danyen mai a cikin gida ba.

Farashin Makamashi Ya Hau

Kasuwannin duniya sun mayar da martani cikin sauri. Rahotanni sun nuna cewa farashin iskar gas ya tashi da kashi 46 cikin 100, yayin da man fetur ya karu da kashi 13, inda ganga guda ke cin dala 82 mafi girman farashi tun bayan rikicin Hormuz a Janairun 2025.

Masana tattalin arziki na gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba da tsananta, za a iya fuskantar karin hauhawar farashi, wanda zai shafi masana’antu, sufuri da rayuwar al’umma a faɗin duniya.

Fargabar Ƙara Ta’azzara Rikici

Yayin da duniya ke sa ido kan matakan da za a dauka a gaba, kasashe masu dogaro da makamashin yankin na nazarin hanyoyin rage tasirin matsalar. Sai dai duk da haka, har yanzu fargaba na karuwa cewa rikicin ka iya faɗaɗa, ya kuma jefa kasuwannin duniya cikin wani sabon yanayi na rashin tabbas.

Rikicin da ya fara a matsayin martani na siyasa, yanzu na girgiza ginshikan tattalin arzikin duniya kuma tasirinsa na iya dadewa fiye da yadda ake zato.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker