Yanzun yanzun INEC ta ce Gwamna Obaseki na PDP ya doke Ize-Iyamu na APC a zaben da a kayi jiya asabar a jihar Edo,
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin takaran sa na Jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu ƙuri’u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 223,619.