NNPC ta samu ₦2.68tr kudin shiga duk da raguwar hako mai

Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya sanar da samun kudaden shiga na Naira tiriliyan 2.68 a watan Fabrairu 2026, duk da cewa yawan man fetur da ake hakowa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.51 a rana kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Rahoton ya nuna cewa duk da karin kudaden shiga da kashi 4.2 cikin ɗari, ribar kamfanin ta ragu sosai da kusan kashi 65 cikin ɗari, inda ta sauka daga Naira biliyan 385 zuwa Naira biliyan 136.
An danganta wannan raguwar riba da karin kudaden da kamfanin ya mayar wa gwamnati bayan cire tsarin rike kashi 30 cikin ɗari na riba.
A bangaren ayyuka, an bayyana cewa raguwar yawan man da ake hakowa ta samo asali ne daga matsaloli da suka haɗa da lalacewar bututun mai da kuma jinkirin gudanar da wasu muhimman ayyuka.
Sai dai rahoton ya nuna cewa samar da iskar gas ya karu sosai a wannan lokaci, duk da cewa sayar da danyen mai ya ragu sakamakon matsalolin fitar da shi zuwa kasuwannin waje.
Haka kuma, samun fetur a gidajen mai na NNPC ya ragu zuwa kashi 58 cikin ɗari, lamarin da ke nuna ƙalubale a bangaren rarraba mai.
A gefe guda, kamfanin ya ce ana ci gaba da manyan ayyukan bututun gas kamar Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK) Gas Pipeline da Obiafu–Obrikom–Oben (OB3) Gas Pipeline, waɗanda suka kusa kammala.





