Labarai

Najeriya na da  yawan masu cutar sikila a duniya – VC

Mataimakin Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor) na Jami’ar Yakubu Gowon, Farfesa Hakeem Fawehinmi, ya bayyana cewa Najeriya ce ke dauke da mafi girman nauyin masu cutar sikila a duniya, inda ake samun kusan yara 150,000 da ake haifa da cutar a kowace shekara.

Farfesan ya bayyana hakan ne a taron kungiyar PACTS kan kula da masu cutar sikila a yankin Afirka ta Kudu da Sahara, wanda aka gudanar karkashin CESRTA a Abuja.

Ya ce yara da dama da ke fama da cutar na fuskantar radadi na rayuwa baki daya, tangardar karatu, karancin damar rayuwa, da kuma rashin samun ingantacciyar kulawar lafiya, musamman a yankunan karkara da gefen birane.

A cewarsa, halin da ake ciki na cutar sikila a Najeriya babbar matsalar lafiya ce da ke bukatar hadin gwiwa daga gwamnati, cibiyoyin bincike da sauran masu ruwa da tsaki domin shawo kanta.

Shi ma Daraktan CESRTA, Farfesa Obiageli Nnodu, ya ce duk da cewa an samar da ka’idojin kula da masu cutar sikila a Najeriya, aiwatar da su a asibitoci har yanzu bai kai yadda ake bukata ba.

Ta ce har yanzu akwai kalubale kamar rashin wayar da kai, tsangwama daga al’umma, nisan asibitoci, da wahalar samun magunguna masu muhimmanci.
A nata bangaren, Farfesa Imelda Bates ta ce yara masu cutar sikila na cikin hadari saboda matsalolin lafiya da zamantakewa, tare da nauyin kudin jinya da ke kan iyalai.

Rahotanni sun nuna cewa kusan daya cikin mutane hudu a Najeriya na dauke da kwayar cutar sikila, abin da ke nuna muhimmancin gwaji da gano cutar da wuri domin ceton rayuka.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker