Musulmai 75 Sun Rasa Rayukansu a Harin Kwara – AbdulRazaq

Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana cewa akalla Musulmai 75 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da aka kai al’ummomin Woro da Nuku a jihar.
Gwamnan ya ce harin ba na ‘yan bindiga ba ne, illa masu tsattsauran ra’ayin addini ne suka kai shi. Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ziyarar da ya kai yankin a daren Laraba.
A cewarsa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura bataliyar sojoji zuwa Kwara domin ɗaukar matakan gaggawa, mayar da martani ga harin, da kuma ƙarfafa tsaro a yankin.
Hukumomin tsaron Najeriya sun danganta harin da ƙungiyar Boko Haram, yayin da fadar shugaban ƙasa ta fitar da wata sanarwa ta ta’aziyya, inda ta la’anci abin da ta kira “mummunan hari na rashin imani.”
Sanarwar ta buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi domin tallafa wa al’ummomin da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa masu hannu a kisan gillar ba za su tsira daga hukunci ba.
Ta kuma bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya nuna matuƙar fushi da alhini kan kisan da aka yi wa mutanen da aka ce an yi ƙoƙarin tilasta musu tsattsauran ra’ayin addini, tare da jaddada cewa dukkan waɗanda aka kashe Musulmai ne.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ma ta yi Allah-wadai da harin, tana mai kira ga hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike mai zaman kansa da adalci, tare da ƙara ƙoƙari wajen kare rayukan jama’a.
Hare-haren tsaro na ci gaba da ƙaruwa a yankin tsakiyar Najeriya, musamman a jihohin Neja da Kogi. A wani hari daban a jihar Katsina da ke arewacin ƙasar, wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutum 21, kamar yadda mazauna yankin da ‘yan sanda suka bayyana.





