Siyasa
Kwankwaso Ya Koma Jam’iyyar ADC

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da komawarsa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a gidansa da ke Kano, inda ya gana da magoya bayansa domin sanar da sabon matakin siyasar da ya ɗauka.
A yayin taron, tsohon gwamnan ya buƙaci magoya bayan tafiyar Kwankwasiyya da su fara yin rijistar shiga jam’iyyar ADC tare da tabbatar da sun mallaki katin zaɓe na ƙasa domin shiga harkokin siyasa a nan gaba.
Karanta Kwankwaso Zai Shiga ADC A Ranar Litinin
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sauye-sauyen siyasa a ƙasar, musamman gabanin shirye-shiryen zaɓukan da ke tafe.





