Kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatarwar sanata natasha

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da dakatarwar da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, bisa zargin rashin da’a, tana mai cewa majalisar ta yi hakan ne bisa tanadin doka.
Kotun, wadda alkalai uku suka saurari shari’ar, ta yanke hukunci cewa dakatarwar ba ta saba wa kundin tsarin mulki ko hakkin majalisa ba, kuma babu hujjar da ta nuna cewa an tauye wa Sanatar wani hakki na doka.
Sai dai kotun ta soke hukuncin raina kotu da kuma tarar Naira miliyan biyar da aka kakaba mata, wanda ya samo asali daga wasikar neman afuwa ta barkwanci da ta aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
A hukuncin da ya jagoranta, Mai shari’a Abba Muhammed ya ce Shugaban Majalisar Dattawa bai yi kuskure ba wajen hana Sanatar damar magana a zaman majalisa na ranar 20 ga Fabrairu, 2025, domin ba ta zauna a kujerar da aka ware mata ba.
Kotun ta jaddada cewa dokokin Majalisar Dattawa sun bai wa Shugaban Majalisa ikon ware kujeru ga ‘yan majalisa, tare da sharadin cewa kowane ɗan majalisa zai iya magana ne kawai daga kujerar da aka tanada masa. A cewar kotun, wannan ya tabbatar da cewa matakin da majalisar ta ɗauka ya kasance bisa doka da ka’ida.





