Labarai

Kotu a Kano Ta Soke Nasarar Abdullahi Ghali Shitu a Kumbotso

Babbar kotu a jihar Kano ta soke nasarar Abdullahi Ghali Shitu a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, tare da tabbatar da hukuncin da ta riga ta yanke a baya, wanda ya ayyana Ali Musa Dan Maliki a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun ta jaddada cewa hukuncin da ta yanke tun ranar 25 ga Oktoba, 2024, yana nan daram, inda ta ce Ali Musa Dan Maliki ne ya cancanci riƙe mukamin bisa tanadin doka.

Masu kare hakkin Ali Musa Dan Maliki ne suka garzaya kotu bayan da Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Abdullahi Ghali Shitu ranar 14 ga Nuwamba, 2024 a matsayin shugaban ƙaramar hukumar.

Da wannan hukuncin, kotun ta umarci dukkan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar da hukuncin ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da bin doka da oda a harkokin mulki a matakin ƙaramar hukuma.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker