Labarai

Jirgin Sama Dake Kan Hanyar Zuwa Rasha Ya Rikito

Jirgin saman fasinja kirar Embraer da ya taso daga Azerbaijan zuwa Rasha ya rikito a kusa da birnin Aktau na kasar Kazakhstan a yau Laraba dauke da fasinjoji 62 da ma’aikata 5, kamar yadda hukumomin Kazakhstan suka sanar, inda suka ce mutane 27 sun tsallake rijiya da baya.

Sanarwar da ma’aikatar agajin gaggawa ta kasar dake tsakiyar nahiyar Asiya ta fitar ta ce, ma’aikatan kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar kuma wadanda suka tsira da rayukansu ciki har da yara 3 na samun kulawa a wani asibitin dake kusa da wurin.

Kamfanin jiragen saman kasar Azerbaijan ya ce an tilastawa jirgin, wanda ya jima yana jigila tsakanin baku zuwa Grozny, babban birnin yankin Chechnya na Rasha, yin saukar gaggawa a wani wuri dake da tazarar kilomita 3 daga birnin Aktau na Kazakhstan.

Kamfanonin yada labaran kasar Rasha sun ce an sauyawa jirgin akala ne saboda yanayin hazo da aka tashi da shi a birnin Grozny.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker