Iran ta kara kai hare-hare kan kasashen yankin Gulf

Iran ta ci gaba da luguden hare-hare ta amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa a kan wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha.
Rahotanni sun nuna cewa an samu irin waɗannan hare-hare da daddare a ƙasashe kamar Qatar, Kuwait da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
A ƙasar Bahrain kuma, kamfanin Alba, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin samar da goran-ruwa (aluminium) a duniya, ya bayyana cewa yana nazarin irin ɓarnar da hare-haren suka yi wa wasu daga cikin masana’antunsa.
Tun da farko Iran ta ce ta kai hari kan wasu masana’antun samar da goran-ruwa a Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta yi zargin cewa wuraren na da alaƙa da sojojin Amurka.
Haka kuma Iran ta yi barazanar kai hare-hare kan jami’o’in da ke da alaƙa da Isra’ila da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin ramuwar gayya ga harin da ta ce an kai wa wasu cibiyoyin iliminta a Tehran.
Dakarun Juyin Juya Halin Iran sun kuma gargaɗi ɗalibai, malamai da mazauna kusa da irin waɗannan jami’o’i da su nisanci harabarsu da tazarar aƙalla kilomita ɗaya domin kare lafiyarsu.
Sun jaddada cewa Iran za ta ci gaba da mayar da martani har sai Amurka ta fito fili ta soki hare-haren bama-bamai da aka kai wa jami’o’in Iran.





