INEC Ta Fitar da Sabbin Ka’idojin Jam’iyyun Siyasa Gabanin Zaben 2027

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, Independent National Electoral Commission (INEC), ta bayyana daftarin sabbin dokoki da ka’idoji na shekarar 2026 da za su jagoranci ayyukan jam’iyyun siyasa gabanin babban zaben 2027.
Shugaban INEC, Joash Amupitan, ne ya sanar da hakan a wani taron tuntuba da shugabannin jam’iyyun siyasa da aka gudanar a Abuja.
Ya ce an sake duba ka’idojin ne bayan amincewa da sabon dokar zabe ta 2026, yana mai cewa Najeriya ba za ta iya tafiya zuwa zaben 2027 da tsoffin ka’idojin 2022 ba.
A cewarsa, sabbin ka’idojin sun hada da tsauraran matakai kan yadda jam’iyyun siyasa za su tafiyar da zaben fidda gwani, kudaden yakin neman zabe, da kuma yadda za a tabbatar da gaskiya da adalci a cikin tsarin siyasa.
Ya kuma bayyana cewa an yi amfani da bayanai daga Political Party Performance Index (PPPI) wajen gano matsalolin da ke tsakanin kundin tsarin jam’iyyu da yadda ake gudanar da su a matakin kasa.
Amupitan ya kara da cewa sabbin dokokin za su inganta tsarin rajistar jam’iyyun siyasa, hadewar jam’iyyu, da kuma gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin gaskiya da bin doka.
Har ila yau, dokokin sun kunshi matakai da za su tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana tare da mutunta haƙƙin ‘yan ƙasa.
Haka kuma, sabbin ka’idojin sun tanadi ma’auni na musamman domin ƙara yawan shigar mata, matasa da kuma masu nakasa a cikin harkokin siyasa.
Shugaban INEC ya bukaci jam’iyyun siyasa da su kalli dokokin ba a matsayin takura ba, sai dai kariya da zai taimaka wajen inganta dimokuraɗiyya.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Inter-Party Advisory Council (IPAC), Yusuf Dantalle, ya bukaci majalisar dokokin kasa da ta sake duba dokar zabe ta 2026 domin guje wa matsaloli gabanin zaben 2027.
Dantalle ya ce wasu tanade-tanaden dokar, musamman wajabta zaben fidda gwani kai tsaye (direct primaries), na iya jefa jam’iyyun siyasa cikin matsin lamba, musamman waɗanda ba su da iko a gwamnati.
Ya kuma soki sharadin da ke bukatar jam’iyyu su gabatar da rajistar mambobinsu tare da lambar shaidar kasa (NIN) a cikin gajeren lokaci, yana mai cewa hakan zai iya hana miliyoyin ‘yan Najeriya shiga harkokin siyasa.
Kazalika, ya bukaci a dawo da tsarin aika sakamakon zabe kai tsaye zuwa dandalin IReV domin tabbatar da gaskiya da amincewar jama’a a zabe.
IPAC ta kuma jaddada bukatar kafa Hukumar Laifukan Zabe domin hukunta masu sayen kuri’u da sauran laifukan zabe a Najeriya.





