Addini

Hukumar Hisbah ta kama mutum tara da ake zargi da karya azumi a Kano

Hukumar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da kama wasu Musulmai tara da ake zargi da cin abinci da rana a ranar farko ta azumin watan Ramadan a Kano.

Rahotanni sun ce an kama mutanen ne a ranar Laraba bayan jami’an hukumar sun gan su suna cin abinci da tsakar rana, lokacin da ake sa ran masu azumi su nisanci hakan.

A duk lokacin Ramadan, jami’an Hisbah kan zagaya kasuwanni da wuraren sayar da abinci domin tabbatar da cewa Musulmai suna bin ka’idojin azumi. Sai dai a wasu sassan birnin, musamman inda Kiristoci da sauran wadanda ba Musulmai ba ke zaune, gidajen abinci kan ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.

Azumi, wanda ke hana cin abinci da sha daga fitowar rana zuwa faduwarta, na daga cikin muhimman ginshikan Musulunci da ke jagorantar rayuwar mabiya addinin.

Mataimakin kwamandan Hisbah, Mujahid Aminudeen, ya shaidawa BBC cewa daga cikin wadanda aka kama akwai mata biyu da maza bakwai.

Ya ce an tsare su ne domin a wayar musu kai kan muhimmancin azumi, tare da koyar da su yadda za su inganta ibada, ciki har da salla da karatun Al-Kur’ani.

Har yanzu ba a bayyana lokacin da za a saki mutanen da aka kama ba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker