Labarai

Harin Makami Ya Hallaka Mutane 4 a Isra’ila

Mutane huɗu sun rasa rayukansu a birnin Haifa bayan wani harin makami mai linzami da ake zargin Iran ta kai. Harindya auku ne a daren Lahadi inda makamin ya bugi wani ginin zama, ya lalata shi gaba daya.

Bayan harin, jami’an ceto sun shafe awanni suna tono baraguzan ginin domin ceto wadanda abin ya shafa. Daga bisani an samu gawarwakin mutum hudu daga karkashin ginin.

Sojojin Isra’ila sun tabbatar da faruwar lamarin, yayin da tashin hankalin ke ci gaba da karuwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Wannan hari na daga cikin jerin hare-haren da ke kara dagula rikicin tsakanin Iran da Isra’ila.

Masana sun bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na iya kara tsananta rikicin yankin, tare da janyo karin asarar rayuka da lalacewar dukiyoyi.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker