Duniya

Gwamnatin Nijar ta ayyana hutun kwanaki 10 na karshen Ramadan ga makarantun Boko

Gwamnatin Jamhuriyar Niger ta sanar da sauyin tsarin hutun Eid al-Fitr, inda ta umarci a rufe dukkan makarantun Boko na tsawon kwanaki goma a karshen watan Ramadan.

Sabon tsarin hutun zai bai wa malamai da dalibai damar samun lokaci mai yawa domin ibada da kuma kammala azumi cikin kwanciyar hankali a duk fadin kasar.

A baya dai hutun karamar sallah a Nijar yawanci bai wuce kwana daya zuwa biyu ba.

Amma a wannan karo, gwamnati ta kara yawan kwanakin hutun domin saukaka wa malamai da dalibai wajen gudanar da ibadunsu a kwanaki na karshe na watan Ramadan.

Daya daga cikin masu fafutukar ganin an samar da wannan sabon tsarin hutu, Abdou Dan Neito, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka matuka wajen ba wa dalibai da malamai damar mai da hankali kan ibada da kuma shirye-shiryen sallar karamar sallah.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker