Kiwon Lafiya

Gwamnatin Jihar Kano Ta Raba Motoci 484 Na Daukar Marasa Lafiya

Gwamnatin kano ta raba motocin daukar marasa lafiya masu kafafu uku guda 484 ga dukkan mazabu a jihar kano.

Gwamnatin Jihar Kano ta raba motocin daukar marasa lafiya masu kafafun uku guda 484 ga dukkan mazabu 484 a kananan hukumomi 44 na jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kaddamar da shirin mai taken “One Ward, One Ambulance,” wanda kuma aka sanya wa suna Abba Gida-Gida Rural Ambulance Service. An kaddamar da shirin ne domin inganta harkokin kiwon lafiya da saukaka kai marasa lafiya asibitoci cikin gaggawa.

Gwamna abba kabir Yusuf ya bayyana cewa an kaddamar da shirin ne domin taimaka wa mata masu juna biyu, yara, wadanda hatsarin mota ya rutsa da su, da sauran mutanen da ke bukatar kulawar gaggawa. Musamman mazauna yankunan karkara. Ya ce an kera motocin ne ta yadda za su iya tafiya a kananan hanyoyi da wuraren da ke da wahalar zirga-zirga, inda manyan motocin asibiti kan samu matsala wajen isa.

Gwamna abba kabir Yusuf ya yi kira ga sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin al’umma da ma’aikatan lafiya da su taimaka wajen kula da motocin. Wannan zai tabbatar da dorewar shirin. Ya jaddada cewa hadin gwiwa ne zai sa shirin ya ci gaba da kasancewa da inganci.

Raba motocin agajin gaggawa 484 wani muhimmin mataki ne na inganta kiwon lafiya a Jihar Kano. Ana sa ran shirin zai ceci rayuka, musamman a yankunan karkara da ke da karancin motocin agajin gaggawa. Kulawa da goyon bayan al’umma shi ne makullin nasarar shirin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker