Gwamnatin Gombe Ta Haramta Sana’ar Jari Bola Saboda Dalilan Tsaro

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da haramta sana’ar jari bola a duk faɗin jihar, a wani mataki da ta ce an ɗauka domin ƙarfafa tsaro da kare dukiyoyin jama’a da na gwamnati.
Matakin ya biyo bayan taron Majalisar Tsaro ta Musamman da aka gudanar tare da manyan jami’an tsaro a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, domin nazarin sabbin ƙalubalen tsaro da wasu abubuwa masu tayar da hankali da aka samu a jihar a baya-bayan nan.
Gwamnatin ta bayyana cewa haramcin ya fara aiki nan take, kuma zai ci gaba da kasancewa har sai an tsara sana’ar jari bola ƙarƙashin shugabanci da kulawa ta musamman.
A cewar gwamnatin, an samu karuwar rahotannin satar kayan more rayuwa da lalata kadarorin gwamnati da na makarantu, inda galibi ake danganta irin waɗannan laifuka da hanyoyin da kayan ke shiga hannun masu sana’ar jari bola.
Majalisar Tsaron jihar ta nuna damuwa mai tsanani kan yadda rashin tsari da shugabanci a cikin sana’ar ke sa wahalar sanya ido, sa ido kan ayyukan masu sana’ar, da kuma tabbatar da bin doka.
Gwamnatin ta ƙara da cewa a nan gaba za ta kafa kwamitin aiwatarwa da sa ido domin tsara harkar yadda ya dace da doka, tare da tabbatar da tsaro da bin ƙa’ida a dukkan ƙananan hukumomi na jihar.





