Labarai

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Ziyarci Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Kasa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara fadar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ke Abuja a yammacin ranar Litinin.

Ziyarar ta gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yada rahotanni game da yiwuwar sauya sheƙarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasa.

A baya-bayan nan, siyasar Kano ta ɗauki sabon salo bayan fitowar waɗannan rahotanni, lamarin da ya jawo martani daga jagororin jam’iyyar NNPP, ciki har da jagoranta kuma uban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, waɗanda suka nuna rashin amincewa da duk wani yunƙuri na sauya sheƙa.

Rahotannin sun kuma haifar da saɓani a cikin jam’iyyar NNPP a jihar, inda aka samu rarrabuwar kai tsakanin magoya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma masu biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Sanata Kwankwaso.

Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnan ko ofishinsa da ke tabbatarwa ko musanta sauya sheƙar da ake ta rade-radin ta.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker