Tsaro

Guinea ta saki sojojin Saliyo 16 da ta tsare a kan iyaka

Gwamnatin Guinea ta saki sojoji da ’yan sandan Sierra Leone guda 16 da ta cafke a yankin iyaka tsakanin kasashen biyu.

An mika jami’an tsaron ga mahukuntan Saliyo ne bayan wata tattaunawar diflomasiyya da aka gudanar a birnin Conakry, tsakanin Ministan Harkokin Wajen Saliyo, Timothy Kabba, da Firaministan Guinea, Amadou Oury Bah.

Sojojin Guinea sun tsare jami’an ne a farkon makon nan bisa zargin cewa sun shiga yankin Guinea ba tare da izini ba a gundumar Koudaya, inda aka ce sun kafa tanti tare da ɗaga tutar kasarsu.

Sai dai gwamnatin Saliyo ta musanta zargin, tana mai cewa jami’an nata na aikin gina ofishin tsaro ne a garin Kaliyereh da ke cikin iyakarta a lokacin da aka kama su.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin na da nasaba da tsohon rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman a yankin Yenga, wanda ya samo asali tun lokacin yaƙin basasar Saliyo.

An tabbatar da cewa dukkan jami’an sun isa birnin Freetown lafiya kalau.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker