Labarai

FRSC Ta Sallami Jami’ai 43 Kan Laifukan Rashin Biyayya da Dabi’a Maras Kyau

Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa (FRSC) ta sallami jami’ai 43 daga aiki bayan an same su da laifukan rashin biyayya da dabi’a maras kyau da suka aikata yayin gudanar da aikinsu.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa daga cikin jami’an da aka sallama, 31 an kore su ne saboda rashin biyayya, 5 saboda dabi’a maras kyau, yayin da 7 kuma aka sallame su saboda aikata laifuka a lokacin sintiri.

Shugaban FRSC, Shehu Mohammed, ya ce matakin wani bangare ne na kokarin tabbatar da cewa jami’an hukumar suna bin ka’idojin aiki da ladabi yadda ya kamata.

Ya jaddada cewa alamar FRSC na nuni da gaskiya, dabi’a mai kyau da jajircewa wajen aiki, yana mai cewa duk wani jami’in da ya saba da dokokin hukumar zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Ya kuma bayyana cewa rashin biyayya babban laifi ne, musamman ga hukumar da ke da alhakin kare rayukan jama’a a hanyoyi. A cewarsa, ɗabi’a maras kyau da aikata laifuka yayin sintiri na rage amincewar jama’a ga hukumar tare da saɓa wa ƙa’idojin da suka ginu kan gaskiya da ladabi.

Hukumar ta kara da cewa za ta ci gaba da karfafa tsarin sa ido da kulawa a cikin gida, tare da wayar da kan jami’anta kan muhimmancin dabi’a mai kyau da bin ka’idoji a dukkan sassan ta a fadin kasa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker