Kasuwanci

Darajar Naira na iya kaiwa N1,100 kan dala a 2026 – Aliko Dangote

Fitaccen dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ana hasashen darajar naira za ta iya karuwa zuwa kusan N1,100 kan dala daya nan da shekarar 2026, matukar sauye-sauyen tattalin arziki da rage dogaro da shigo da kaya daga kasashen waje suka ci gaba da tafiya yadda ake fata.

Dangote ya yi wannan bayani ne yayin kaddamar da wani shiri da ya shafi bunkasa masana’antu na shekarar 2025, inda ya jaddada muhimmancin karfafa samar da kayayyaki a cikin gida domin rage bukatar dalar Amurka daga kasashen waje.

A cewarsa, alamun farfadowar naira da ake gani a ‘yan makonnin nan na da alaka da manufofin gwamnati na karfafa masana’antu, da kuma rage shigo da kayayyaki daga waje  musamman man fetur da sauran muhimman kayayyaki.

Ya kara da cewa ci gaba da aiwatar da wadannan matakai zai taimaka wajen karfafa tattalin arziki, daidaita kasuwar musayar kudi, tare da ba naira damar samun karin karfi a nan gaba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker