Dan Bello Ya Sha Alwashin Bincike Akan Sarkin Misau, Ya Bukaci Jama’a Su Tura Masa Da Bayanai

Masanin harkokin siyasa da zamantakewa kuma sanannen mai shirya bidiyo na barkwanci da siyasa, Dan Bello, ya bayyana aniyarsa ta kaddamar da bincike kan Sarkin Misau, Ahmed Suleiman (wanda ya masa lakabi da Amadu Mugu), bisa zarge-zargen da ake ta yi masa a kafafen sada zumunta.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Dan Bello ya bukaci mabiyansa da su rika tura masa duk wasu bayanai da suke da su game da dukiyoyin Sarkin Misau, inda ya ke samun kudade, kasashen da ya kan ziyarta, da kuma kadarorin da ake zargi ya mallaka.

“Duk wanda ya san wani abu akan Amadu Mugu Sarkin Misau ya turo ta inbox. Gidaje, filaye, plaza, gonaki, kasashen da yake zuwa, inda yake samun kudi – turo mu bincika. A saki Yakubu nan take! Ku cigaba da turowa, za mu bincika,” in ji shi.
Dan Bello ya kuma zargi Sarkin da barin wasu jami’ai su doke wani talaka har suka jefa shi kurkuku, saboda ya nuna rashin amincewa da manufofinsa.
Ya kara da cewa akwai zarge-zarge masu yawa da suka shafi cin zarafin al’umma da kuma wasu badakalar da suka shafi matasa da dalibai a wasu makarantu a Misau wanda ya hada da Zargin yiwuwar cin zarafin yara da lalata da wasu matasa, ciki har da dalibai a Kwalejin A.D. Rufai na Koyon Shari’a da Jami’ar Bauchi Gadau acewar wani bayani da aka tura masa;.

“Mara martaba Amadu Mugu na Misau, ashe akwai zarge-zarge. Za mu bude sabon file mai kauri,” in ji Dan Bello, yana mai nanata bukatarsa ta a saki Yakubu nan take!
Hausa360 ta tuntubi wasu daga cikin mutanen Misau, inda suka bayyana cewa ya kamata hukumomi su dauki matakin da ya dace idan akwai gaskiya a cikin wadannan zarge-zargen, amma kuma a tabbatar da bin doka da adalci wajen gudanar da bincike.
haka kuma A wata majiyan mu na Hausa360 cewar ana sa ran gwamnatin Bauchi zata dauki matakin bincike da kuma tabbatar da hukuncin da ya dace.
Wannan batu ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta, inda jama’a ke cigaba da tura bayanai da kuma bayyana ra’ayoyinsu game da zarge-zargen da ake yi.
Kulura: wannan rahoto na dauke da bayanan da suka fito ne daga zarge-zargen jama’a a kafafen sada zumunta. Babu wani hukunci na kotu ko sakamako na hukuma da ke tabbatar da sahihancin wadannan maganganu tukuna. Don haka, za a iya kallonsa a matsayin labarin da zai ya ci gaba zuwa nan gaba bayan abubuwan da ke faruwa. Hukumar Hausa360 za ta ci gaba da bincike, kuma za mu sabunta wannan labari idan an samu karin bayani daga majiyoyi masu inganci. ya kamata jama’a su dauki wadannan bayanai a yanda yake kuma har sai hukumomi sun gudanar da cikakken bincike, ba za a iya yanke hukunci akaiba.





