COVID-19: Gomnan jihar Bauchi ya tattauna kai tsaye da al’ummar jiha ta wayar hanu
Gomna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi yau, yayi jawabi wa al’ummar jiha kan Chutar COvid-19 daganan yagana da Al’ummar jihar ta wayar tan garaho.
Gomnan wadda yagana da yan’jarida kai tsaye a Gidajen radio na jiha, yace bamujin dadin yadda al’ummah suke wahala musamman wadda suka zabemu daga matakina kasa saboda matakan da Gomnati ta dauka na kare yaduwar chutar COvid-19 a jihar.
Yakuma ce zasuyi aiki don antabbatar dacewa za’ayi dukkan mai yuyuwa don aga antaimaka don ganin anshawo matsalolin dasuka damemu.
Yace, a yanxu Gomnatin jiha ta samarda wuri da gadodi daza’a kwantar da Marasa lafiya guda 500 don kwanatar da masu dauke da chutar COvid-19
Yakuma, tabbatar wa Garuruwar da aka killacesu dacewa Gomnatinsa zata Samar musu da abinci karkashin Kwamitin tallafa da rage radadin’ na COvid-19 a Wanann lokaci.
Gomna Bala Muhammad Abdulkadir yabayyana wasu matakai da Gomnati tadauka don ganin antare yaduwar chutar, duka matakan dazamu dauka yayi dai-dai dana hukumomin duniya ne.
Gomnan yayi anfani da wannan damar yabayyana wa al’ummah yawan muce mucen da aka samu a karamar Hukumar Azare, wadda shine hedkwata na Katagum, yace mutum 150 ne suka mutu a cikin wata daya’ Kuma bayada hadi da chutar COvid-19.
Yakuma, jaddada aihin Umurnin fara aiki da Abun rufe baki da hanci (face mask) dakuma wanke hanu da (hand sanitizer) don kashe chutar.
Gomna Bala Muhammad Abdulkadir wadda ya amsa tambayoyi da dama ta wayar tarho daga al’ummar jihar, musamman na ganin andauki wasu matakai , dakuma bada shawara da tsokaci duk anyi.
Gomnan yace zaiyi wani Kwamiti wadda zai duba yadda baza’a dunga uxira wa al’ummah ba ko ci musu zarafi ba bisa ka’ida ba, zasu Kuma wayar wa jama’a kai da irin tsare tsaren Gomnati data shigo dasu don yaki da chutar a jihar yadda yadace.
Wadda sukayi magana a Tattaunawar sun hada’ Kwamishinan Lafiya, Dr. Aliyu Maigoro da Shugaban Hukumar lafiya ta jiha, Dr Rilwanu Muhammad.
Ofishin babban Maitallafawa Maigirma Gomna kan yada’labarai Comrade Mukhtar Gidado