Labarai

Bauchi Ta Cika Shekaru 50, Gwamna Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai da Kishin Kasa

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bukaci al’ummar jihar da su kwaikwayi sadaukarwa, ladabi da jajircewar iyayen da suka assasa jihar, yayin da Bauchi ke bikin cika shekaru 50 da kafuwa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a cikin jawabin da ya gabatar ga al’ummar jihar baki ɗaya domin tunawa da bikin Golden Jubilee na kafuwar Jihar Bauchi.

A cewarsa, ci gaban Bauchi a ƙarni na 21 zai dogara ne sosai kan ingancin shugabanci da kuma irin nauyin da ’yan jihar ke ɗauka a matsayinsu na ’yan ƙasa masu kishin ci gaban al’umma.

Bala Mohammed ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na shimfiɗa tubalan ci gaba masu ɗorewa, inda ya ce hakan ya yi daidai da Tsarin Tattalin Arzikinsa na My Bauchi Project da kuma Babban Tsarin Ci Gaban Jihar.

“Mu a matsayinmu na gwamnati, muna nan daram wajen gina tubalan ci gaba masu ƙarfi da za su dore bayan mu, bisa tsarin tattalin arzikimmu na My Bauchi Project da kuma ajandar ci gabanmu kamar yadda ke kunshe a cikin Tsarin Ci Gaban Jihar,” in ji shi.

Gwamnan ya gode wa ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da suka aiko da saƙonnin taya murna tare da halartar bukukuwan, inda ya taya al’ummar Bauchi murnar cika shekaru 50 da kafuwar jihar.

“Ina taya mu duka murnar wannan babban tarihi na cika shekaru 50 da kafuwar jiharmu mai albarka,” in ji shi.

Ya bayyana bikin Golden Jubilee a matsayin wani muhimmin lokaci a tarihin Bauchi, yana mai cewa bikin na bukatar zurfin tunani kan tafiyar jihar zuwa yanzu, godiya ga sadaukarwar da aka yi a baya, da kuma sabunta alkawari na gina makoma mai kyau tare.

“Cikar Jihar Bauchi shekaru hamsin da kafuwa, wadda daga cikinta aka samar da Jihar Gombe a shekarar 1996, babban abin farin ciki ne kuma abin godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki. Duk da ƙalubalen siyasa, tattalin arziki da zamantakewa, Jihar Bauchi ta daure tare da samun cigaba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Hakika, dorewar wata jiha tsawon shekaru hamsin tare da ci gaba a hankali babban nasara ce da ta cancanci biki da tunani.”

Gwamnan ya jaddada cewa kafuwa da dorewar Jihar Bauchi tun daga shekarar 1976 ya samu ne sakamakon hangen nesa da sadaukarwar iyayen da suka assasa jihar.

“Waɗannan jarumai masu kishin ƙasa sun shimfiɗa tubalan mulki nagari, haɗin kai da ci gaba da jihar ke kai a kai a yau. Muna girmama tarihinsu tare da roƙon Allah Ya gafarta wa waɗanda suka riga mu gidan gaskiya,” in ji shi.

Bala Mohammed ya kuma yaba da gudummawar tsofaffin shugabanni da suka jagoranci jihar a lokacin mulkin soja da na farar hula, tun daga gwamnan soja na farko, Kanal Muhammad Bello Kaliel, zuwa gwamnan farar hula na farko, Alhaji Abubakar Tatari Ali.

Haka kuma, ya yi karrama ga marigayi Shugaban Ƙasa, Janar Murtala Ramat Mohammed, wanda ya ƙirƙiri Jihar Bauchi a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, tare da wasu jihohi shida daga tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas.

Rahotanni sun nuna cewa sauran shugabannin da suka mulki jihar sun haɗa da marigayi Janar Garba Duba, marigayi Manjo Janar Muhammad Sani Sami, Manjo Janar Chris Abutu Garuba, marigayi Manjo Janar Joshua Madaki, marigayi Kanal Abu Ali, marigayi Alhaji Dahiru Mohammed, marigayi Wing Cmdr. James Yana Kalau, Navy Capt. Adisa Raji, Kanal Theophilus Bamigboye, Wing Cmdr. Adamu Mishelia, Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu, Malam Isa Yuguda, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, da kuma gwamna mai ci Bala Abdulkadir Mohammed.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker