Siyasa

APC Ta Bukaci Nyesom Wike Ya Ajiye Muƙaminsa na Ministan Abuja

Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Bashiru, lamarin da ya kai ga jam’iyyar APC kiran da Wike ya sauka daga muƙaminsa na minista, bisa hujjar cewa ba mamba ba ne a jam’iyyar.

Sakataren jam’iyyar ya bayyana wannan matsaya ne bayan Wike ya gargade shi da ya janye daga tsoma baki a siyasar Jihar Ribas, musamman bayan sanarwar da shugabancin APC suka fitar cewa Gwamna Siminalayi Fubara shi ne jagora kuma shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Wike ya yi tir da matakin jam’iyyar, yana mai cewa tsoma bakin shugabannin APC a siyasar Ribas na iya haddasa rikici da ruɗani a jihar.

Rikicin ya samo asali ne tun bayan ziyarar da Ajibola Bashiru da tawagarsa suka kai wa Gwamna Siminalayi Fubara a Jihar Ribas. Bayan ziyarar, Bashiru ya sake jaddada matsayar jam’iyyar APC cewa kowane gwamna shi ne jagoran jam’iyyar mai mulki a jiharsa, tsarin da ya ce jam’iyyar ke mutuntawa a faɗin ƙasar.

Wannan cacar-baka na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa da fafatawa tsakanin manyan ’yan siyasa, lamarin da ke nuna ƙara tsananta rikicin siyasa a Jihar Ribas da ma matakin ƙasa baki ɗaya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker