An tallafawa Yara Masu Zanga Zangar Yinwa da Tsadar Rayuwa Da Naira Miliyan 2
Jama’a Sun Tallafawa Yara Yan Kano Masu Zanga-Zangar Yinwa da Tsadar Rayuwa Da Naira Million 2
A yau Laraba Bar. Abba Hikima lauyan Al’umma da kare hakkin dan Adam ya sanar da samun taimako daga jama’a ga ƙananan yara waɗanda aka kama domin gudanar da zanga-zangar Yinwa da Tsadar Rayuwa da ya addabi ƙasa. Wannan taimako ya biyo bayan yanci da suka samu daga tsarewar da aka yi musu bayan sun shaki iskar yanci.
Mutane da dama, ciki har da manyan malamai, da Mawaka, sun tallafa wa waɗannan yara domin tabbatar da suna da wani tallafi wajen sake rayuwa. Wasu sun bayar da gudummawar miliyoyi, yayin da masu karamin karfi suma suka bayar da nasu guduma ta hanyar turawa asusun Banki na A. A. Hikima & Co. dake Jaiz wanda Bar. Abba Hikima ke Jagoranta.
Daga cikin waɗanda suka bayar da tallafin akwai Prof. Ibrahim Maqari da ya bayar da N1,000,000 da kuma Alhaji Naziru Sarkin Waka wanda shima ya bada tallafin N1,000,000 ta hannun wakilinsa. Sauran sun hada da Hajiya Samira Ado da Muhammad Abdullahi Sulaiman da dai sauran ‘yan ƙasa masu kishin al’umma.