
Dubban alhazai daga sassa daban daban na duniya sun taru a Dutsen Arfah domin gudanar da daya daga cikin manyan rukunnan aikin Hajjin shekarar 2026.
Tun daga safiyar ranar, mahajjata suka fara isa filin Arfah cikin natsuwa da ibada, inda suka kasance suna addu’o’i, karatun Alkur’ani da neman gafarar Allah.
Mahukuntan Saudiyya sun dauki matakai masu yawa domin tabbatar da tsaro da walwalar alhazan, tare da samar da motocin daukar marasa lafiya, ruwa da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Haka kuma jami’an lafiya da masu aikin agaji sun bazama domin taimaka wa mahajjatan da suka fito daga kasashe daban daban.
A yayin zaman Arfah, alhazai sun bayyana farin cikinsu da samun damar halartar aikin Hajji cikin kwanciyar hankali.
Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa wannan rana tana daga cikin mafi muhimmanci a rayuwarsu saboda dimbin falalar da take tattare da ita.
Bayan kammala zaman Arfah, mahajjatan za su nufi Muzdalifah domin ci gaba da sauran ayyukan Hajji, ciki har da jifan jamarai da yankan hadaya.
Hajjin bana ya gudana cikin tsari da lumana, yayin da mahajjata ke ci gaba da gudanar da ibadunsu cikin nutsuwa da biyayya.





