Siyasa

NDC ta tsayar da Gawuna a dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

Jam’iyyar NDC ta kammala tantancewa tare da tsayar da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Bayanin hakan ya fito ne daga taron da shugabannin jam’iyyar suka gudanar a Kano, inda aka ce an zaɓi Gawuna ne bisa la’akari da gogewarsa a siyasa, kwarewarsa a shugabanci, da kuma tasirin da yake da shi a fadin jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ta ce tana da yakinin cewa Gawuna zai iya wakiltar yankin Kano ta Tsakiya yadda ya kamata, tare da kawo sauye-sauye a fannin wakilci da ci gaban al’umma.

An kuma bayyana cewa matakin na NDC na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar na ƙarfafa ƙwazo a fagen siyasar Kano gabanin babban zaɓe na 2027.

Sai dai har yanzu ba a samu cikakken martani daga Dr. Nasiru Yusuf Gawuna kan karɓar takarar ba a lokacin da aka fitar da wannan rahoto.

Za a ci gaba da bibiyar yadda al’amura za su kaya yayin da siyasar Kano ke ƙara ɗaukar zafi gabanin 2027.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker