Isra’ila ta kashe mutane 9 a kudancin Lebanon

Israel ta kai hare-hare a kudancin Lebanon inda ta kashe akalla mutane tara, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, wacce aka tsawaita kwanan nan.
Hukumar labaran Lebanon (NNA) ta ce harin da aka kai a garin Jebchit ya kashe mutane uku tare da jikkata bakwai, yayin da a Toul aka kashe hudu tare da jikkata shida. A Harouf kuma mutane biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wani gida ya rushe.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren Isra’ila sun kara tsananta a ‘yan kwanakin nan, inda aka yi luguden wuta a wasu garuruwa da dama a kudancin Lebanon, ciki har da Zawtar al-Sharqiyah, Yohmor al-Shaqif da Bayt al-Sayyad.
A cikin awanni 24 da suka gabata, hare-hare ta sama sun kashe sama da mutane 20, ciki har da iyalai biyu, sojojin Lebanon biyu da kuma ma’aikatan jinya uku, yayin da sama da mutane 70 suka jikkata.
Haka kuma, sojojin Isra’ila sun fitar da sabbin umarnin korar jama’a daga garuruwa 15 na kudancin Lebanon, lamarin da ya kara tayar da hankali a yankin.
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce kudancin Lebanon zai fuskanci makoma irin ta Gaza, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi da Hezbollah.
A nasa bangaren, shugaban Lebanon, Joseph Aoun, ya yi Allah-wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai cewa hare-haren suna kara yawan mutuwa da barna a kowace rana.





