Yanbindiga sun kashe mutum 10 a Kebbi

Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya sun nuna cewa ƴanbindiga sun kai hari wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Shanga, inda suka kashe fiye da mutum 10.
Ana zargin maharan na da alaƙa da ƙungiyar ƴanmahmuda. Sun mamaye garuruwa da dama ciki har da Kawara, lamarin da ya tilasta wa al’ummar yankin tserewa zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
Wani da ya tsere zuwa daji ya shaida wa BBC cewa yara na fama da yunwa da ƙishi yayin da suke ɓoye a cikin dajin.
Haka kuma wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun shigo ne daga jihar Neja, inda suka ƙona gidaje da dama tare da lalata dukiyoyi. An kuma ce maharan na fakewa a wani dutse da ke kusa da garin Kawara.
Shugaban ƙaramar hukumar Shanga ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa an tura wani kwamiti zuwa yankin domin duba halin da ake ciki, duk da cewa yankin na ƙetaren ruwa ne kuma yana da wahalar isa.





