Labarai

ADC  Ta Yi Allah-Wadai da Hare-Haren Yan Bindiga a Katsina

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Katsina ta yi kakkausar suka kan sabbin hare-haren yan bindiga da ke faruwa a yankuna daban-daban na jihar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa kashe jami’an tsaro da fararen hula abin damuwa ne kwarai, tare da cewa lamarin ya wuce matakin da za a yi shiru akai.

ADC ta bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen dakile ayyukan yan bindiga, tare da samar da tsare-tsare masu dorewa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Hare-haren yan bindiga a Arewa maso Yamma na ci gaba da zama babban kalubale, inda al’ummomi da dama ke fuskantar matsalar tsaro, garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Jam’iyyar ta jaddada cewa dole ne a dauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen wannan matsala kafin ta kara ta’azzara.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker