Rivers: An Kashe Naira Biliyan 302 a Watanni Shida

Rivers: An Kashe Naira Biliyan 302 a Watanni Shida
gwamnatin jihar ribas ta bayyana cewa an kashe sama da Naira biliyan 302 cikin watanni shida a lokacin mulkin tsohon mai kula da jihar Ibok Ete Ibas (Rtd), daga Maris zuwa Agustan 2025.
An bayyana hakan ne a takardun kotu da aka gabatar a Babbar Kotun jihar da ke Port Harcourt, sakamakon karar da Socio Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta shigar domin neman gaskiya kan yadda aka kashe kudaden gwamnati.
Rahoton ya nuna cewa jihar ta samu kusan Naira biliyan 298.35, inda Naira biliyan 253.48 suka fito daga FAAC, yayin da sauran Naira biliyan 44.87 suka fito daga wasu hanyoyi. Sai dai jimillar kudin da aka kashe ta zarce Naira biliyan 302.35.
An kashe sama da Naira biliyan 112.4 kan albashi, fansho da sauran kudade, yayin da aka ware Naira biliyan 163.4 ga ma’aikatu da hukumomi, inda sama da Naira biliyan 106 aka kashe a watan Agusta kadai.
Haka kuma, an kashe sama da Naira biliyan 26 wajen biyan bashi, tare da kusan Naira miliyan 491 kan kudin banki. Rahoton ya kuma nuna cewa an rika tura kudade zuwa gidan gwamnati daga Naira miliyan 1.8 zuwa biliyan 4.27.
Abin lura shi ne, an amince da kashe Naira biliyan 28 domin girka CCTV amma ba a kashe kudin ba.
SERAP ta ce tana ci gaba da nazarin takardun domin sanin ko za a bukaci karin bayani ko daukar mataki. An dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga Mayu, 2026.





