Siyasa

APC Ta Fitar da Farashin Fom din Takarar Zaben 2027

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana farashin fom din da masu sha’awar tsayawa takara za su saya domin fafatawa a zaɓen shekarar 2027.

A cewar bayanin da aka fitar, farashin fom ɗin ya bambanta gwargwadon mukamin da ɗan takara ke neman tsayawa, inda mukamin shugaban ƙasa ke da mafi tsada.

Ga jerin farashin fom ɗin kamar haka:

  • Shugaban Ƙasa: Naira miliyan 200
  • Gwamna: Naira miliyan 150
  • Sanata: Naira miliyan 100
  • Majalisar Wakilai: Naira miliyan 70
  • Majalisar Dokokin Jiha: Naira miliyan 20

Matakin fitar da farashin fom ɗin na daga cikin shirye-shiryen jam’iyyar domin fara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Karanta: APC Ta Zabi Sabbin Shugabanninta

Masu lura da al’amuran siyasa sun bayyana cewa wannan tsari na iya kara nuna irin karfin tattalin arziki da ake buƙata ga ‘yan takara da ke son shiga manyan muƙaman siyasa a ƙasar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker