Labarai

“Babu Yan Bindiga a Abuja” — Wike Ya Karyata Zargin Rashin Tsaro

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa babu yan bindiga da ke aiki a Abuja, duk da cewa ana samun wasu kananan laifuka a birnin.

Wike ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa game da tsaro a babban birnin tarayya habuja, inda ya ce bai kamata a dauki kowane lamari guda daya a matsayin babban barazana ba.

A cewarsa, babu wani wuri a duniya da ba a samun laifi, har ma a kasashe masu ci gaba, amma hakan ba yana nufin akwai yan bindiga ko kungiyoyin ta’addanci ba.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake mayar da hankali ga munanan abubuwa kadai ba tare da yabawa kokarin da hukumomi ke yi wajen rage laifuka ba.

Ministan ya kara da cewa Abuja birni ne mai bude kofa wanda ke jawo mutane daga wurare daban-daban, amma hakan ba yana nufin akwai tsari na yan bindiga a ciki ba.

Sai dai wannan bayani na Wike ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da muhawara kan tsaro a kasar, musamman bayan hare-haren bam da suka afku a Maiduguri, inda mutane da dama suka rasa rayukansu tare da jikkata wasu.

Duk da haka, ya jaddada cewa hukumomi za su ci gaba da inganta tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker