Labarai
Kotu ta yanke wa Samha M Inuwa hukuncin daurin wata shida

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta yanke wa jarumar Kannywood Samha M Inuwa hukuncin daurin wata shida a gidan yari bayan samunta da laifin wulakanta takardar naira.
A makonni biyu da suka gabata, jami’an EFCC sun kama jarumar bayan wani bidiyo ya nuna tana watsa majina kan takardar naira 1,000 abin da aka ɗauka a matsayin take dokar kudi ta CBN ta shekarar 2007, sashe na 21.
Rahoton Daily Nigerian ya ce an gurfanar da ita a gaban kotu bisa zargin, inda ta amsa laifin tare da roƙon sassauci, tana mai cewa wannan ne karo na farko da aka same ta da irin wannan laifi.
Alkalin kotun, M.S Shuaibu, ya yanke mata hukuncin daurin wata shida, tare da ba ta zaɓin biyan tarar naira 200,000 maimakon zaman gidan yari a Najeriya.





