IPOB Ta Soke Dokar Zaman Gida Ta Kowane Litinin A Gabashin Najeriya

Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya sanar da soke dokar zaman gida da ake aiwatarwa duk ranar Litinin a fadin gabashin Najeriya, inda dokar za ta daina aiki daga Litinin, 9 ga Fabrairun 2026.
Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful, ya fitar ta bayyana cewa Kanu ya bayar da umarnin ne domin bai wa dalibai damar komawa makaranta, tare da bai wa ‘yan kasuwa da sauran hukumomi a yankin Igbo damar gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci ba tare da tsangwama ba.
Sanarwar ta kara da cewa duk wanda ke da shakku kan sahihancin wannan umarni, zai iya ziyartar gidan yarin da Nnamdi Kanu ke tsare a jihar Sokoto domin jin hakan kai tsaye daga bakinsa.
IPOB ta jaddada cewa duk wani mutum ko kungiya da ke kira da a ci gaba da dokar zaman gida, suna bijire wa umarnin Kanu, kuma za a dauke su a matsayin masu adawa da ci gaban yankin gabashin Najeriya.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa babu wani gwamna da ke da hurumin yin barazanar rufe ko lalata kasuwanci, inda kungiyar ta yi gargadi cewa za ta mayar da martani ga Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, ko duk wani gwamna da ya yi irin wannan barazana.
A gefe guda kuma, bidiyon da aka fitar na wasu dakarun IPOB da ake zargi da tilasta aiwatar da dokar zaman gida, sun tabbatar da cewa an soke dokar a sauran sassan Najeriya.





