Labarai

CUPS Ta Kaddamar da Sabon Logo

Kungiyar Citizens United for Peace and Stability (CUPS) ta fitar da sabon tambarinta wanda aka ce ya lashe gasar zane na kungiyar. Dr. Idris Ahmed, shugaban kungiyar, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau, 9 ga watan Janairu, 2025.

Bayan nazari mai zurfi da aka gudanar kan tambarin da aka gabatar, kungiyar ta bayyana cewa tambarin da matashin mai zane, Adamu Muazu Mijinyawa, ya kirkira, shi ne ya samu nasara. An bayyana cewa bai yi amfani da wata fasahar artificial intelligence (AI) wajen kirkirar wannan tambari ba.

CUPS ta yi kira ga mabiya da masu goyon baya da su yi amfani da wannan tambarin wajen tallata sunan kungiyar a rubuce-rubucensu da kuma kafafen sada zumunta.

Kungiyar ta ce kare martaba da bunkasa sunan CUPS yana da matukar muhimmanci wajen cimma burin ceton Arewa da al’ummarta. Dr. Idris ya ce:

“Muna rokon Allah Ubangiji ya albarkaci wannan kuduri da nasara mai tarin yawa. Amin, Ya Rabbi.”

Ana fatan wannan sabon tambari zai kara fito da matsayin CUPS a matsayin wata kungiya mai karfin gwiwar kawo zaman lafiya da daidaito a yankin Arewa da ma duniya baki daya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker