Jerin Sunayen Yan Siyasa Daga Arewa Da Ake Sa Ran Zasu Takarar Shugabancin Kasa A 2027
Zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027 ya na ƙara ƙaratowa, kuma hasashen waɗanda za su tsaya takarar kujerar mulki daga arewacin Najeriya ya fara fitowa fili. Ga wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa biyar daga yankin da ake hasashen za su nemi goyon bayan jama’a don kujerar shugabancin ƙasa.
1. Kwankwaso (Rabiu Musa Kwankwaso)
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP. Kwankwaso ya kasance fitaccen dan siyasa mai farin jini musamman tsakanin matasa da talakawa. Ana ganin yana da damar cika gurbin shugabanci idan ya samu goyon baya sosai daga arewa.
2. Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP na zaɓen 2023. Atiku, wanda ya fito daga Adamawa, yana da dogon tarihi a siyasar Najeriya tare da gogewar da ka iya ba shi damar sake neman kujerar shugabancin ƙasa.
3. Malam Nasiru El-Rufa’i
Tsohon Gwamnan Kaduna kuma tsohon Ministan Birnin Tarayya, El-Rufa’i na daga cikin wadanda ake ganin suna da kwarewa da kuma tasiri a harkokin mulki. Ra’ayoyinsa masu tsauri sun jawo masa farin jini da kuma adawa a lokaci guda.
4. Hamza Almustapha
Fitaccen tsohon babban jami’in soja wanda ya kasance kusa da tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha. Almustapha ya shiga siyasa da niyyar kawo sauyi ga Najeriya, inda yake jan hankalin jama’a da manufofinsa na tabbatar da tsaro da adalci.
5. Sanata Bala Mohammed (Ƙauran Bauchi)
Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya. Bala Mohammed yana da gogewa a harkar mulki da tasirin siyasa, musamman a yankin arewa maso gabas. Ana ganin yana cikin masu ƙwarin gwiwar tsayawa takara a 2027.
Wa Ya Kamata A Marawa Baya?
A yayin da ake hasashen waɗannan sunaye, tambayar ita ce: wa ya dace ‘yan arewa su marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa? Shin zaɓi zai kasance kan gogewa, farin jini, ko manufofi?
Jama’a na ci gaba da bayyana ra’ayinsu kan waɗannan sunaye tare da fatan ganin wanda zai kawo ci gaba mai dorewa ga Najeriya. Ku kasance tare da Hausa360 don samun sabbin labarai akan wannan batu.