Labarai
Trending

Jihar Bauchi za ta samar da karin hanyoyi Bogoro zuwa Lusar da kuma Boi zuwa Tampshin

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya rattaba hannu kan cikon kasafin kudin shekarar 2020 wanda ya haura Naira biliyan arbain da biyu da zai bada dama wa gwamnati gina karin hanyoyin sufuri.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya rattaba hannu kan cikon kasafin kudin shekarar 2020 wanda ya haura Naira biliyan arbain da biyu da zai bada dama wa gwamnati gina karin hanyoyin sufuri.

Da yake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Bala Muhammad yace gwamnatinsa karkashin kasafin za ta samar da karin hanyoyin sufuri a fadar jiha da sauran shiyyoyi uku dake jihar Bauchi.

Hanyoyin da za’a samar sun hada da:

  • Hanyar Bogoro zuwa Lusar
  • Boi zuwa Tampshin a shiyyar Bauchi ta Kudu.

Sauran sun hada da hanyoyi biyu a kowace shiyyar Arewa da Tsakiyar jiha.

Gwamnan sai yayi amfani da damar wajen yabawa majalisar dokoki ta jiha kan goyon baya da hadin kai da take bayarwa wajen nasarar gwamnatin sa.

Gwamna Bala sai ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da kammaluwar hanyoyin da ma sauran ayyukan da ta bayar akan lokaci.

Shima a nasa tsokacin, kakakin majalisar dokoki ta jiha Hon Abubakar Suleiman cewa yayi majalisar a nata bangaren za ta cigaba da marawa gwamnatin baya don inganta jiha.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker