An soke rundunar SARS a Najeriya
Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a Najeriya wato SARS.
Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye ga manema labarai a ranar Lahadi.
Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar, inda ko a yau Lahadi sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila.
‘Yan ƙasar dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.
A baya dai gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.