Kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa don tantance ma’aikata da kuma binciko wadanda basu da lambar BVN ya mika rahoton sa ga Gwamna Bala Muhammad inda suka ce sun taskance kimanin Naira miliyan dari biyu da ashirin da biyar da dubu dari biyar.
Da yake mika rahoton shugaban kwamitin Sanata Ibrahim yace Gumba sun gano ma’aikatan bogi da kuma masu karbar albashi sama da daya.
Yace tun farko kwamitin ya dukufa wajen tantance ma’aikata sama da dubu arba’in da kuma wasu masu karbar fansho cikin jadawalin biyan albashin gwamnatin jiha.
Sanata Gumba yace manufar kafa kwamitin shine tsaftace aikin gwamnati tare da tabbatar da ma’aikatan dake karbar albashi halastattu ne.
Gwamna Bala Muhammad da ya bayyana gamsuwar sa kan kwazon membobin kwamitin da ya bayyana su a matsayin kwararru.
Ya yabawa aikin nasu tare da alkawarin aiki da rahoton su don inganta aikin gwamnati.
Gwamnan sai yayi amfani da damar wajen rarrashin ma’aikatan wadanda binciken ya rutsa da su tare da basu tabbacin cewa albashin duk wadanda aka tabbatar da su na nan kuma za’a biya su a kowane lokaci.