Zelenskyy ya zargi Putin da haddasa rikicin da zai iya kaiwa Yakin Duniya na Uku

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana wa BBC cewa takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, ya riga ya kaddamar da abin da ya kira Yakin Duniya na Uku, yana mai kira da a kara matsin lambar soja da tattalin arziki kan Moscow.
A hirar da aka yi da shi gabanin cika shekaru hudu da mamayar da Rasha ta kai wa kasarsa, Zelenskyy ya zargi Putin da yunkurin kafa sabon tsarin rayuwa a duniya. Ya kuma yi gargadi cewa hare-haren ba za su tsaya kan Ukraine kadai ba idan ba a dakatar da shi ba.
Ya ce kasarsa ba za ta yi rashin nasara ba domin tana yaki ne don kare ‘yancin cin gashin kanta. A cewarsa, duk da tsawon lokacin rikicin, Ukraine na tsaye daram kuma ba ta rasa ikon mallakar kanta ba.
Shugaban ya kara da cewa rikicin ya jawo asarar rayukan dubban daruruwan mutane, ciki har da fararen hula, tare da haddasa matsaloli ga tattalin arzikin duniya.
Ya jaddada cewa dole ne kasashen duniya su kara hadin kai wajen daukar matakan da za su hana rikicin ya kara fadada, yana mai cewa matsin lamba na hadin gwiwa shi ne hanya mafi inganci ta dakile barazanar.




