Labarai

Yan takarkaru sun tabbatar APC jam’iyya ce mai dimokuradiyya — Yilwatda

Nentawe Goshwe Yilwatda, shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce yadda ake bai wa masu neman takara damar sayen fom domin fafatawa da Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin jihohi, ya tabbatar da cewa APC ita ce jam’iyya mafi dimokuradiyya a Najeriya.

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai bayan duba yadda ake sayar da fom din takara a Abuja ranar Laraba, inda ya ce babu wani shiri na tsawaita wa’adin sayar da fom din.

Ya bayyana jin dadinsa da yadda tsarin ke tafiya cikin sauki ba tare da wata matsala ba, yana mai cewa babu wanda aka hana sayen fom din takara.

A cewarsa, yadda ‘yan takara ke zuwa suna sayen fom har ma da masu kalubalantar shugaban kasa da gwamnoni, na nuna irin karfin dimokuradiyya da kuma karbuwar jam’iyyar.

Ya kuma ce babu korafi daga masu takara ko a ofis ko a kafafen sada zumunta, yana mai cewa APC na kokarin samar da ingantaccen aiki ga mambobinta.

Yilwatda ya kara da cewa idan aka yi la’akari da yadda komai ke tafiya cikin lumana, jam’iyyar na da yakinin samun nasara a zaben gaba.

Game da yiwuwar kara lokaci, ya ce akwai jadawalin ayyuka, kuma duk wani sauyi sai an bi ka’ida tare da shawarar kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC), amma a halin yanzu babu wani karin lokaci.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker