Venezuela na shirin sakin fursunoni — sabuwar afuwa ta gwamnati

Delcy Rodríguez, shugabar gwamnatin rikon kwarya ta Venezuela, ta rattaba hannu kan wani kuduri na afuwa ga wasu fursunoni matakin da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka ce zai iya rage radadin da daruruwan fursunonin siyasa ke ciki.
Rahotanni sun nuna cewa ana hasashen fursunonin siyasa a kasar sun kai kusan 600, sai dai har yanzu ba a bayyana adadin mutanen da za su amfana da afuwar ba.
Masu fafutika sun bayyana cewa afuwar ba za ta shafi wadanda aka samu da laifin jagorantar tawaye, rashawa, ko kuma wallafa sakonnin da gwamnati ta ɗauka a matsayin adawa a kafofin sada zumunta ba.
Matakin na iya shafar fitattun ‘yan adawa, ciki har da María Corina Machado, wadda gwamnatin ƙasar ta zarga da neman goyon bayan kasashen waje, zargi da ya kara tsananta rikicin siyasa da ke tattare da shugabancin Nicolás Maduro.
Masu sharhi na ganin cewa wannan afuwa na iya zama wani yunkuri na rage matsin lamba da kuma sassauta rikicin siyasa da ke addabar kasar a halin yanzu.





