UAE Ta Karyata Zargin Taimaka wa RSF da Makamai a Sudan

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta musanta zarge-zargen da ke cewa ta samar da makamai tare da taimakawa wajen jigilar kayan yaki ga dakarun Rapid Support Forces (RSF) a Sudan.
A wata sanarwa da ta fitar, UAE ta bayyana cewa ba ta tura “kowane irin makami, harsashi, jirgi mara matuki ko wani kayan yaki” ga RSF ba.
Wannan martani na zuwa ne bayan wasu rahotannin jaridu sun yi zargin cewa kasar ta taimaka wajen horar da mayakan RSF tare da ba su tallafin dabaru da kayan aiki.
UAE ta kuma jaddada cewa ba ta da hannu a rikicin Sudan, kuma ba ta shiga cikin wani bangare na yakin da ake yi a kasar.
Yakin basasar Sudan ya barke ne a watan Afrilun 2023, sakamakon rikici tsakanin Rundunar Sojojin Sudan (SAF) da RSF. Duk da kokarin sasanci da Amurka da Saudiyya ke jagoranta a birnin Jeddah, har yanzu ba a kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa ba.





