Troy Deeney Ya Fitar da Jerin Team of the Week na gasar Premier league

Troy Deeney ya bayyana yan wasan da suka fi taka rawar gani a gasar Premier League, inda Bruno Fernandes da Anthony Gordon suka fito fili.
Shahararren mai sharhi kan kwallon kafa na BBC, Troy Deeney, ya fitar da jerin yan wasan da suka fi taka rawar gani a makon nan na gasar Premier League.
A cikin jerin, mai tsaron raga Aaron Ramsdale ya samu yabo bayan rawar da ya taka wajen taimakawa kungiyarsa samun nasara a kan Chelsea.
A bangaren tsakiya, Bruno Fernandes ya yi fice bayan ya karya tarihin assists na kulob din, inda ya zarce na David Beckham.
Haka kuma, Dominik Szoboszlai, William Saliba da Konstantinos Mavropanos sun taka rawar gani a bangarensu.
A gaba kuwa, Anthony Gordon ya ci gaba da nuna bajinta wajen zura kwallaye, yayin da matashin dan wasa Max Dowman ya ja hankali da kwazon da ya nuna.
Haka kuma, matashin dan wasa Rio Ngumoha ya burge da yadda yake kai hari kai tsaye ga abokan hamayya.
A bangaren masu horarwa, kocin Newcastle United, Eddie Howe, shi ne aka zaba a matsayin kocin mako bayan nasarar da kungiyar ta samu a kan Chelsea duk da kalubalen wasannin da suka biyo baya.
Jerin ya nuna yadda ‘yan wasa daban-daban ke taka rawar gani a gasar, tare da hada manya da matasa masu tasowa a fagen kwallon kafa.





