Labarai

Tinubu Ya Nada Taiwo Oyedele a Matsayin Ministan Kudi

Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nad a Taiwo Oyedele a matsayin Karamin Ministan Kudi, inda zai maye gurbin Doris Uzoka-Anite.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan.

A cewarsa, Uzoka-Anite za ta koma Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Tarayya wato Federal Ministry of Budget and National Planning inda za ta yi aiki a matsayin Karamin Minista, wanda shi ne matsayi na uku da ta rike a wannan gwamnati.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika sunan Oyedele ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa da shi, ta hanyar wasiƙa da aka aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Kafin nadin nasa, Oyedele, wanda ya fito daga garin Ikaram a yankin Akoko na Ondo State, shi ne shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Haraji da Gyaran Tsarin Haraji, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen sauya tsarin haraji na Najeriya.

Oyedele mai shekaru 50 kwararre ne a fannin tattalin arziki, lissafi da manufofin gwamnati.

Ya yi karatu a Yaba College of Technology inda ya samu Higher National Diploma (HND) a fannin lissafin kuɗi da harkokin kudi. Daga baya ya samu digirin farko a fannin Applied Accounting daga Oxford Brookes University.

Haka kuma ya halarci shirye-shiryen karatu na manyan makarantu irin su London School of Economics, Yale University, Gordon Institute of Business Science da kuma Harvard Kennedy School.

Oyedele ya shafe shekaru sama da 22 yana aiki a kamfanin PwC inda ya shiga aiki a shekarar 2001 kuma ya kai matsayin Fiscal Policy Partner da Africa Tax Leader.

A halin yanzu, shi farfesa ne a Babcock University sannan kuma visiting scholar a Lagos Business School.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker