Siyasa

Sameera Abubakar Ta Halarci Tantancewar APC A Abuja

Amb. Dr. Sameera Abubakar Abdullahi, yar takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kabo da Gwarzo, ta halarci zaman tantance ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa halartar tantancewar na zuwa ne bayan kiraye-kirayen al’ummar yankin da ke nuna goyon baya ga takararta, sakamakon irin gudummawar da take bayarwa wajen ci gaban al’umma da ayyukan raya kasa.

An bayyana Dr. Sameera a matsayin daya daga cikin fitattun mata masu taimakon marasa galihu, musamman yara kanana, mata, masu karamin karfi da kuma masu bukata ta musamman.

Baya ga ayyukan jin kai, tana kuma taka muhimmiyar rawa a bangaren kasuwanci da bunkasa tattalin arziki a matakin jiha da kasa baki daya.

Masu goyon bayanta sun bayyana fatan ganin ta samu nasara a takarar domin ci gaba da kawo ayyukan alheri da cigaba ga al’ummar Kabo da Gwarzo.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa fitowar Dr. Sameera a siyasar majalisar wakilai na kara jawo hankalin mata da matasa a yankin gabanin zabukan 2027.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker