Pa Onyebgule daga jahar Imo Najeriya ya cika shekaru 128

An gudanar da gagarumin biki a kauyen Obazu da ke karamar hukumar Mbaitoli a jihar Imo State, yayin da wani dattijo da ake kyautata zaton shi ne mafi tsufa a Najeriya ya cika shekaru 128 da haihuwa.
Dattijon mai suna Anthony Anyiam Onyebgule ya cika shekarunsa ne a ranar Litinin, 9 ga Maris, inda gidansa ya zama tamkar wurin ziyara yayin da jama’a daga wurare daban-daban ke tururuwa domin ganinsa da taya shi murna.
Har yanzu yana tafiya da kansa
Rahotanni sun nuna cewa duk da yawan shekarunsa, Pa Onyebgule har yanzu yana iya tafiya da kansa ba tare da taimako ba, kuma yana gudanar da wasu ayyukan yau da kullum kamar karatu da wanka ba tare da taimakon wasu ba.
Abin da ya fi bambanta shi da sauran tsofaffi shi ne siririn jikinsa, amma har yanzu yana da kwakwalwa mai kyau ba tare da wata alamar mantuwa ko cutar Dementia ba.
Wanda ya gano shi ya shirya bikin
Wanda ya gano dattijon kuma ya shirya masa bikin haihuwar shi ne Chidiebube Okeoma, wanda shi ne shugaban gidauniyar Stand for Humanity Foundation.
Okeoma ne ya dauki nauyin dukkan kudaden bikin da aka gudanar a gidan dattijon a kauyen sa.
Da yake magana da manema labarai, Okeoma ya bayyana farin cikinsa da gano dattijon, yana mai cewa yana ganin rayuwarsa a matsayin wata babbar albarka daga Allah.
“Ina matuƙar farin ciki cewa ni ne na gano wannan dattijo wanda ake ganin shi ne mutum mafi tsufa a duniya. Ina fatan Allah ya ba ni irin tsawon rai da lafiyar da ya samu,” in ji shi.
Kira ga gwamnatin jihar Imo
Okeoma ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Imo State karkashin jagorancin gwamnan jihar Hope Uzodimma da ta girmama dattijon ta hanyar sanya sunansa a wani babban aikin gwamnati.
Ya ce hakan zai zama wata hanya ta girmama rayuwar dattijon da kuma nuna muhimmancin irin wannan tarihi ga al’umma.
Abin mamaki ga mutane da dama
Mutane da dama da suka halarci bikin sun bayyana mamakinsu ganin dattijon da ya rayu fiye da karni guda, inda wasu ke ganin hakan wata babbar shaida ce ta tsawon rai da lafiya.
Wasu ma na ganin idan aka tabbatar da shekarunsa, Pa Onyebgule na iya kasancewa daga cikin mutane mafi tsufa a duniya.





