Labarai

Najeriya Ta Dauki Kamfanin Amurka Don Karyata Zargin Kisan Kiristoci

Gwamnatin Najeriya ta ɗauki hayar wani kamfani daga ƙasar Amurka domin taimaka mata wajen karyata rahotannin da ke cewa ana kashe Kiristoci kaɗai a hare-haren ƴan ta’adda da ke faruwa a wasu sassan ƙasar.

Tun a watan Nuwambar bara ne tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke da matuƙar damuwa, sakamakon abin da ya bayyana a matsayin kisan Kiristoci da ake yi a ƙasar.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, tana mai cewa tana ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai wajen yaƙar mayaƙan IS da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke kai hare-hare kan fararen hula, ba tare da la’akari da addini ba, inda Musulmi da Kirista ke faɗawa hannu ɗaya.

A wani ɓangare na yunƙurin magance wannan cece-kuce, Najeriya ta kashe dala miliyan 4 da dubu 500 wajen ɗaukar hayar kamfanin DCI na Amurka na tsawon watanni shida, domin taimaka mata wajen fayyace gaskiyar lamarin da kuma karyata ra’ayin cewa Kiristoci ne kaɗai ake kai wa hari.

Daga bisani, gwamnatin ta sake biyan ƙarin dala miliyan 4 da dubu 500 domin tsawaita wa’adin yarjejeniyar da kamfanin zuwa ƙarin watanni shida, wanda ya sa jimillar lokacin yarjejeniyar ta kai shekara guda.

Wadannan bayanai na kunshe ne a shafin intanet na Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Disambar bara.

Har zuwa yanzu, kamfanin DCI da gwamnatin Najeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da rahoton da ya bayyana a jaridun ƙasar a ranar Laraba.

A cewar yarjejeniyar, kamfanin DCI zai taimaka wa Najeriya wajen warware batun zargin kisan Kiristoci, tare da tallafa mata wajen ci gaba da samun goyon bayan Amurka a yaƙin da take yi da mayaƙan da ke ikirarin jihadi da sauran ƴan ta’adda a yankin yammacin Afirka.

Idan za a iya tunawa, a watan Disambar bara ne Amurka ta kai wani hari a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, da hujjar kai farmaki kan mayaƙan IS da ke kashe Kiristoci. Daga bisani, shugaba Donald Trump ya amince cewa Musulmi ma na cikin waɗanda hare-haren ƴan ta’adda ke shafa a sassan ƙasar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker