Mutane 37 Sun Mutu Sakamakon Fitar Iskar Gas a Wani Mahakar Ma’adinai a Filato

Akalla masu hakar ma’adinai 37 sun rasu sakamakon fitar iskar carbon monoxide a wani wurin hakar ma’adinai da ke kauyen Kampani Zurak, a cikin Wase Local Government Area na Plateau State.
Wani mai hakar ma’adinai a yankin, Safiyanu Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sama da mutum 20 sun jikkata, kuma an garzaya da su asibiti a garin Wase domin samun kulawa.
A cewarsa, lamarin ya faru da misalin karfe 6:30 na safiyar Laraba, bayan da ma’aikatan suka dawo wurin aiki daga sallar asuba, inda suka gamu da fitar iskar gas din ba zato ba tsammani.
Ya bayyana cewa iskar carbon monoxide ce ta bazu a wurin, ta kashe mutane da dama da suka je neman abin rufa wa kansu asiri. Ya kara da cewa da safiyar ranar, ma’aikatan sun bar wurin don sallah suna raye, amma da suka dawo aka same su cikin wannan hali.
Haruna ya kuma ce babu wani aikin ceto nan take, domin wadanda ake sa ran za su iso da safe domin aiki ba su iso wurin ba a lokacin da lamarin ya faru. An tabbatar da mutuwar mutum 37, yayin da fiye da 20 ke karbar magani a asibiti.
Ana ci gaba da gudanar da sallar jana’izar mamatan a cikin al’umma.
Har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sai dai mazauna yankin sun ce shugaban ƙaramar hukumar ya halarci sallar jana’izar.





